10 Janairu 2022 - 14:56
​Iraki Ta Karbi Fursunonin IS 50 Daga Syria

Iraki ta bayyana cewa, dakarun tsaronta sun karbi fursunoni 50 ‘yan asalin kasar Iraqi wadanda mayakan kungiyar masu da’awar kafa daular musulunci ta IS ne da Syrian ta damke su.

An mika fursunonin ne ta hanyar kan iyakar Rabia dake lardin Nineveh a arewacin kasar Iraki, karkashin jagorancin tawagar dakarun tsaron hadin gwiwa na Iraqi (JOC) da bangaren Syrian.

Sanarwar ta ce, hukumar leken asiri da bincike ta ma’aikatar harkokin cikin gidan Iraki ne ta karbi fursunonin domin daukar matakan shara’a a kansu.

Da ma dai Irakin ta sha karbar rukunonin fursunoni ‘yan asalin kasar Iraki daga bangaren Syria a lokuta da dama wadanda ke da alaka da mayakan IS da aka kama a Syria.

A shekarar 2014, mayakan IS sun yi ikirarin kafa dauloli dake karkashin ikonsu a yankunan kasashen Iraki da Syria, sai dai an kashe dubban mambobin dake biyayya ga kungiyar IS tare da kama wasu bayan kwace ikon yankunan da kungiyar ke rike da su a Iraki a shekarar 2017 daga bisani kuma kasar Syria.

342/